Shugaban na kurdawa a Syira Hikmat al-Hijri ya soki halayyar gwamnatin rikon kwarya ta kasar Syria, tare da nuna kin amincewa da sabon tsarin mulkin kasar da aka sanar kwanaki kadan da su ka gabata.
Hikmata al-Hijri ya yi kira da gyara yadda ake tafiya a yanzu da kuma rubuta sabon tsarin mulki wanda zai zama yana wakiltar dukkanin bangarorin mutanen kasar.
Shugaban na ‘yan Duruz ya bayyana cewa; sabon tsarin mulkin da aka gabatar yana nuni ne da mahangar wani bangare daya na al’ummar kasar, wanda kuma yake share fage na kafa tsarin kama-karya, maimakon kafa tsarin demokradiyya. Haka nan kuma ya ce, ko kadan ba a yi aiki da tsarin da zai kai ga kafa hukuma ba, sannan kuma gwamnatin rikon kwarya ta yi watsi da abinda al’ummar kasar suke son cimmawa ta hanyar juyin da su ka yi.
Dangane da taron kasa da aka yi, shugaban ‘yan Duruz din ya ce, taro ne na sa’o’i 5 kadai wanda kuma ba musayar ra’ayi aka yi ba, an gabatarwa da mahalartarsa umarni ne na abinda ake son yi, don haka gwiwar mutane ta yi sanyi.
Haka nan kuma shugaban na Kurdawa ya zargi kungiyar “Tahrirus-Sham’ da cewa ta damfarawa al’ummar Syria shugabanninta wadanda ba kwararru ba ne, haka nan kuma an kori ma’aikatan gwamnati da dama daga aiki cikin tilasci.
Akan abinda ya faru a gabar ruwan Syria shugaban na ‘yan Duruz ya dorawa gwamnatin alhaki, yana mai yin tuni da cewa, laifukan da aka tafka sun yi kama da wadanda “ Da’esh’ ta aikata.