Sayyid Abul-Malik al-Houthi shugaban kungiyar Ansarallah na kasar Yemen ya bayyana cewa mamayar Karin waurara a cikin kasar Siriya wanda sojojin HKI suka yi kuma suke kara yi wata alamace ta kafa kasar Isra’ila babba.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Al-Houthi yana fadar haka a jiya Alhamis a jawabin mako-mako day a saba yi tun bayan fara yakin tufanar Aksa a shekara ta 2023 da ta gabata.
Shugaban ya kara da cewa HKI tana da wani shiri wanda take kira ‘Hanyar annabi Dawuda’ wanda yake bukatar ta kara mamaye Karin kasashen larabawa don cimma manufarta ta kafa Isra’ila babba.
Shugaban ya kara da cewa a halin yanzu al-amarinn ya zo mata da sauki saboda kasar Amurka tana mamaye da wasu yankuna a gabacin kasar Siriya kusa ta kogin Furat, sannan kungiyar yan ta’adda ta KASAD tana mamaye da yankin kurdawa na kasar Siriya tana bukatar kara mamaye wasu Karin kilomitoci kawai ta cika gurinta da mamar kogin furat.
Shugaban ya bayyana cewa wargaza makaman kasar Siriya da take yi don cimma wannan burin ne, ya kuma aibata sabbin shugabannin kasar Siriya wadanda suka kyale HKI tana mamaye kasar kuma tana lalata makaman kasar ba tare da ta tabuka wani abu ba.