Shugaban Amurka Ya Samu Damar Shimfida Munanan Muradun Kasarsa Kan Sabuwar Gwamnatin Siriya

Bukatun da shugaban Amurka ya fara gabatarwa shugaban gwamnatin Siriya al-Julani a gamuwarsu ta farko Fadar shugabanci ta Amurka White House ta bayyana cikakken bayani

Bukatun da shugaban Amurka ya fara gabatarwa shugaban gwamnatin Siriya al-Julani a gamuwarsu ta farko

Fadar shugabanci ta Amurka White House ta bayyana cikakken bayani kan ganawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Siriya, Ali al-Julani, a birnin Riyadh fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar Laraba.

A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta ce: Trump ya karfafa al-Julani da yin abin da ya bayyana a matsayin wani babban aiki ga al’ummar Siriya, wato sanya hannu kan yarjejeniyar kyautata alakar jakadanci da gwamnatin yahudawan sahayoniyya, a karkashin tsarin da kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Morocco suka kulla alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila a shekara ta 2020.

Trump ya kuma yi kira ga al-Julani da ya kori Falasdinawa daga Siriya, yana nufin manyan shugabannin kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinu.

Trump ya kuma yi kira ga al-Julani da ya yi aiki don hana sake bullowar kungiyar ta’addanci ta Da’ish wato ISIS a Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments