Shugaban Amurka Na Kan Hanyarsa Ta Zuwa Kasar Saudiya

Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudia a wani tafiya ta musamman don samar da kuded da kuma harkokin kasuwa

Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudia a wani tafiya ta musamman don samar da kuded da kuma harkokin kasuwa ga Amurka a yankin Gabas ta tsakiya.

Trump  zai ziyarci wasu kasashen larabawa a yankin, wadanda suka hada da Qatar da HDL da kuma Turkiya inda ake saran zai tattauna dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine tare da shugaban  kasar Turkiyya Rajab Tayyid Urdugan.

Shugaban yana zuwa yankin ne a dai-dali lokacinda HKI ta ci gaba da kissan kiayashi ga Falasdinawa a Gaza da kuma hana abinci shiga Gaza.

Shugaban ya sami labarin saken wani ba’amerike mai suna Edan Alezander wanda yake tsare a hannun kungiyar Hamas tun shekara ta 2023. Kungiyar Hamas ta sake shi ne don ganin HKI ta bude kofar Rafah don a shigo da kayakin abinci ga falasdinawa wadanda suke fama da yunwa. Tun kimani watanni biyu da suka gabata.

Shugaban yace yana saran kulla yarjeniyoyi na zuba jari a Amurka da kuma harkokin kasuwanci a wannan tafiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted