Masar : Al Sisi Ya Ce Zai Sauka Bayan Wa’adin Mulkinsa

Bugu da kari, Sisi wanda yake Magana a bikin yaye sabbin jami'an soja ya kuma ce; Daga yanzu ba za a sake sauya kundin tsarin
alsisi

Shugaba Abdul Fattah al-Sisi ya sanar da cewa zai sauka daga kan karagar mulkin kasar daga nan zuwa shekara ta 2030.

A jiya Asabar ne dai shugaban kasar ta Masar ya yi wannan sanarwar yana bayyana matsayar tashi da cewa yankakken mataki ne.

Bugu da kari, Sisi wanda yake Magana a bikin yaye sabbin jami’an soja ya kuma ce; Daga yanzu ba za a sake sauya kundin tsarin mulkin kasar ba.”

” Zangon karshe na wa’adanin 2030 shi ne zai zama karshen mulkina a matsayin shugaban kasa,idan har ina raye. Wannan wani  yankakken mataki ne da babu tantama akai.”

Bugu da kari shugaban kasar ta Masar ya kara da cewa Za a yi amfani da wannan damar domin tarbiyyantar da wasu sabbin shugabanni.”

Sisi dan shekaru 71 tsohon janar ne na soja wanda ya zama shugaban kasa daga 2014 a karkashin wa’adin Mulki na shekaru hudu. Sai dai daga baya an sauya tsarin mulkin kasar da ya sa aka tsawaita wa’adin mulkin zuwa shekaru 6, haka nan sake bayar da dama a gare shi ya sake tsayawa Takara.

Sai dai a wannan karon ma ‘yan adawa suna shakkun cewa akan cewa abu ne mai yiyuwa a sake sauya tsarin mulkin kasar domin ba shi damar sake tsayawa takara fiye da shekarar 2030.

A tsawon shekaru 12 na mulkinsa al-Sisi ya mayar da hankali wajen yin manyan ayyukan raya kasa, da masu adawa su ka ce ya yi su ne a karkashin ciyo basuka daga waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted