Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon na nan da karfinta, duk da asarorin da ta yi da kuma sadaukarwa.
A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al Manar, Sheikh Qassem ya bayyana cewa, ‘yan gwagwarmaya a kasar Lebanon sun yi nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta kawo karshen hare-haren da Isra’ila a lokacin da suke kara jajircewa.
Ya jaddada cewa “a koyaushe ana ci gaba da tuntubar juna tsakaninsu da shugaban majalisar Nabih Berri, kuma ba mu yi wata tattaunawa a cikin rauni ba.”
Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, muddin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ci gaba da mamayar yankunan Lebanon, to dole ne a tunkare ta ta hanyar gwagwarmaya da ayyukan soji.
Shugaban na Hizbullah ya yi nuni da cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Isra’ila da Lebanon a fili take, babu wata boyayyiyar yarjejeniya da aka kulla, komai a bayyane yake.
Ya yi nuni da cewa, yarjejeniyar ta yi magana karara a kan “kudancin kogin Litani” sau biyar, yana mai cewa, “Wannan shi ne tsarin da ya kamata mu bi.”
“Wannan yarjejeniya wani bangare ne na kuduri mai lamba 1701 na Majalisar Dinkin Duniya na dakatar da ta’addancin Isra’ila,” in ji shi.
Ya ce; “Isra’ila” ta ci gaba da kai hare-hare lokaci-lokaci kan yankunan Lebanon tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki a ranar 27 ga Nuwamba, 2024.
Ko da yake tun da farko an shirya sojojin mamaya na Isra’ila su kammala janyewarsu daga Lebanon a watan Janairu, amma an kara wa’adin zuwa ranar 18 ga watan Fabrairu, amma sun ci gaba da zama a wurare biyar da suke ganin “masu mahimmanci”.