Search
Close this search box.

Sheikh Qassem: An Bude Wani Sabon Shafi Na Gwagwarmaya Da Isra’ila

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya ce a halin yanzu, kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta shiga wani sabon mataki na yaki da

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya ce a halin yanzu, kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta shiga wani sabon mataki na yaki da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.

Da yake jawabi ga dimbin jama’ar da suka taru a wannan  Lahadi domin jana’izar wasu manyan kwamandojin kungiyar Hizbullah a kudancin birnin Beirut, mataimakin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah  ya ce, gwagwarmaya ta shiga  shiga wani sabon mataki a yaki da Isra’ila.

“Barazana ba za ta hana mu ci gaba da abin da muke yi ba,  A shirye muke mu fuskanci dukkan kalubale daga sojojin Isra’ila, ” in ji shi.

Sheikh Qassem ya ce; Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana neman dukaknin hanyoyi ne domin gurgunta masu adawa da zaluncinta, amma mayakan Hezbollah sun kawo karshen wannan mafarkin.”

Sheikh Qassem ya yi nuni da yadda Amurka ke da hannu dumu-dumu a yakin kisan gillar da Haramtacciyar Kasar Isra’ila  ke yi  a zirin Gaza, yana mai cewa Washington ita kanta babban bangare ne na wannan yaki.

Ya yi gargadin cewa gwamnatin Isra’ila za ta ginawa kanta kabarinta da kanta sakamakon ayyikan ta’accinta, za ta rusa tattalin arzikinta, sannan kuma ba za ta cimma burinta ba.”

Sheikh Qassem ya bayyana matakin soja na gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a matsayin “mafi girman matakin aikata laifukan yaki da dabbanci” da ba a taba ganin irinsa a cikin shekarun nan ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments