Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikn Na’im Kassim ya bayyana cewa; Idan har gwamnatin kasar ta gajiya wajen yin abinda ya rataya a wuyanta na tilasta wa ‘yan mamaya aiki da tsagaita wutar yaki, to gwgawarmaya tana da wata hanyar da za ta yi aiki da ita akan ‘yan mamaya.
Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya danage da zagayowar cikar shekaru 25 daga korar ‘yan sahayoniya daga kasar Lebanon da gwgawarmaya ta yi, ya jaddada cewa; “Gwagwarmaya ba za ta yi shiru ba, ba kuma za ta mika wuya ba, tana yin hakuri ne saboda ta bayar da Karin lokacin,don haka ya zama wajibi a yunkura.”
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Gwamnati ce mai hakkin ganin an yi aiki da tsagaita wutar yaki a Lebanon, amma idan gwamnatin ta kasa, to da akwai mafita a hannun gwgawarmaya.”
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; Aikin gwgawarmaya shi ne kare kai, da kuma kin mika kai ga ‘yan mamaya, wani lokaci tana yaki, wani lokacin kuma tana takawa ‘yan mamaya birki, ko ta yi hakuri tana jira amma tana cikin shiri.”
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce, makami ana yin amfani da shi ne bisa dacewar maslaha.”
Wani sashen na jawabin sheikh Na’im Kassim ya kunshi cewa; A wurin gwagwarmaya har yanzu yaki bai kare ba, kuma abinda Isra’ila take yi, yana karawa gwgawarmaya karfi ne da tsayin daka.”
Haka nan kuma ya ce; Kamar yadda babu wanda ya isa ya kawar da Lebanon, babu wanda kuma zai iya kawar da gwagwarmaya daga Lebanon.