Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana Shahidin al’umma Sayyid Hassan Nasrallah da cewa, jagora ne na musamman na al’ummun larabawa da musulmi kuma shugaban gwgawarmaya.
A cikin jawabin da ya gabatar a lokacin jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, da Shahid Hashim Safiyuddin, inda ya bayyan cewa: A wannan rana muna yin ban kwana da jagora na tarihi na musamman wanda kuma yake a matsayin alkiblar ‘yantattun na duniya. Sheik Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah ya kasance wanda ‘yan gwgawarmaya suke kauna, wanda Falasdinu da birnin Kudus ne manufarsa, ya kuma taka rawa wajen farfado da batun kare hakkokin Falasdinawa.
Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid Shahid Hassan Nasrallah ya narke a cikin yi wa musulunci hidima da kuma a cikin riko da wilaya, ya kuwa yi shahada ne a sahun gaba na fagen daga, kuma zai ci gaba da zama a cikin zukatanmu da ruhinmu, za kuma mu yi riko da amana mu ci gaba da tafiya akan wannan tafarkin.
Shekih Na’im Kassim wanda ya yi Magana da sayyid Nasrallah, ya ce: Kai ne kake fadin cewa, tare za mu kammala wannan tafiyar,ko da kuwa za a kashe mu baki daya. Ya Sayyid Nasrallah muna nan akan wannan alkawalin.”
Sheikh Kassim ya kuma ce; Taron da aka yin a jana’iza, yana a matsayin bayyana ra’ayi ne akan riko da gwagwarmaya wanda irinsa ya yi karanci a tarihin Lebanon.