Sheik Na’im Kassim:  Babu Dalilin Ci Gaba Da Zaman Sojojin Mamaya A Lebanon

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi da marecen jiya Lahadi inda ya tabo  muhimman  batutuwa da su

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi da marecen jiya Lahadi inda ya tabo  muhimman  batutuwa da su ka shafi kasar ta Lebanon da kuma yammacin Asiya.

Sheikh Na’im Kassim ya ce wajibi ne ‘yan sahayoniya su janye sojojinsu daga kudancin kasar ta Lebanon domin babu wani dalili na cigaba da zamansu.

Shekih Na’im Kassim ya bayyana ranar 23 ga watan nan na Febrairu ta jana’izar Shahid Sayyid Hassan  da kuma shahid Hashim Safiyuddin a  matsayin ranar jaddada mubaya’a ga tafarkin da ya tafiyar da rayuwarsa a kansa da shi ne gwgawarmaya.

Babban makatakardar kungiyar ta Hizbullah dai ya gabatar da jawabi ne na tunawa da jagororin Hizbullah da su ka gabata, inda ya yi kira da al’ummar kasar da su fito domin halartar jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah.

Sheikh Na’im Kassim ya ce; Ina yin kira ga al’ummarmu da su fito sosai domin halartar jana’izar shahidai, Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Shahid Sayyid Hashim.”

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma bayyana cewa duk wanda yake  son yin matsin lamba akan Hizbullah domin ya raunanata, to ya kwana da sanin cewa ba zai sami nasarar yin hakan ba.

Dangane da batun hana jirgin saman Iran sauka a filin saukar jiragen sama na Beirut, saboda barazanar HKI,  babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kirayi gwamnatin kasar ta Lebanon da ta sauya matsayar da ta dauka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments