Kasar Tunisiya ta shiga cikin sabuwar dambaruwar siyasa saboda yadda ake yi wa wasu fitattun ‘yan siyasa, lauyoyi da kuma ‘yan jarida 40 shari’a, bisa zargin cewa suna yi wa kasa makarkashiya.
An jibge jami’an tsaro masu yawan gaske a bakin kotun, yayin da a wajenta kuma masu fafutuka suke bayar da taken nuna kin amincewa da shari’ar, suna bayar da taken; ‘Neman ‘ ‘yanci, da kuma zargin ma’aikatar shari’a da zama ‘yar koren gwamnati.
Lauya a cikin kwamitin lauyoyi masu bayar da kariya ga wadanda ake yi wa shari’ar, Lamia Farhani ta bayyana cewa; Abin ban mamaki shi ne shugaban kasa wanda ya rantse zai kare shari’a, wanda kuma shi kwararre ne akan tsarin mulki shi ne na farkon da ya karya doka.
Wani daga cikin ‘yan kasa da su ka halarci gangamin mai suna Ahlem ya shaida wa kamfanin dillancin labaurn “Associated Press” cewa; Ya zo ne domin ya nuna goyon bayansa ga wadanda ake tsare da su, tare da tuhumar gwamnatin kasar da cewa garkuwa take yi da mutanen da take yi wa shari’a.
Sai dai kuma wasu ‘yan kasa suna da ra’ayin da yake cin karo da wannan, suna ganin cewa wadanda ake yi wa shari’an sun cancanci a daure su tsawon rai. Har ila yau ya kuma tuhumi ‘yan siyasar da ake yi wa shari’ar da cewa, sun ruguza tattalin arzikin kasar ta yadda darajar kudaden kasar ta fadi kasa.
A gefe daya MDD ta yi kira ga gwamntin ta Tunisiya da ta kawo karshen duk wata shari’a ta siyasa da ake yi wa ‘yan hamayya, sannan kuma ta bar mutanen kasar cikin ‘yancin bayayna ra’ayoyinsu.
MDD ta ce, yi wa ‘yan hamayyar shari’a zai mayar da tsarin demokradiyyar kasar baya.