Sharhin Bayan Labarai Ranar Alhamis

Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan Allah wadai da gwamnatin Siriya ta yi da matakin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar

Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan Allah wadai da gwamnatin Siriya ta yi da matakin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka kan kasarta na kai hare-haren zalunci kan garin Palmyra da ke tsakiyar kasar, tana mai jaddada cewa, hakan yana nuna matakan tsokana na yahudawan sahayoniyya da nufin kunna wutar tashe-tashen hankula a yankin, da ni Sunusi Wunti zan jagoranci gabatar muku da shirin kamar haka:-

Kasar Siriya ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan matakan zaluncin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta daukan kanta ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri kan kasarta musamman na baya-bayan nan kan birnin Palmyra da ke tsakiyar kasar, tana mai jaddada cewa hakan yana nuna munanan matakan laifukan da yahudawan sahayoniyya ke ci gaba da dauka ne kan kasashe da al’ummomin yankin Gabas ta Tsakiya.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata munanan laifuka da cin zarafin kasar Siriya, inda suka kai mummunan harin wuce gona da iri kan birnin Palmyra, inda suka  yi sanadin shahadan mutane 36 tare da raunata wasu da dama, kuma sun kai hare-haren ta hanyar jirgin saman yakin rundunar sojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida. Kuma jirgin saman yakin ya yi luguden wuta ne kan gine-ginen gidajen zaman jama’a ne da suke cikin birnin Palmyra, lamarin da ya haifar da babbar illa ga gine-ginen da aka kai musu hare-haren da na yankuna da suke makwabtaka da yankin.

Sanarwar ta kara da cewa: Jamhuriyar Larabawa ta Siriya ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan wannan danyen aikin, wanda ke nuni da ire-iren muggan laifukan da yahudawan sahayoniyya suke ci gaba da yi kan kasashe da al’ummomin yankin.

Bayanin ya ci gaba da cewa: Kasar Siriya ta tabbatar da cewa, laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa a kan kasashen Siriya da Lebanon da Falastinu a matsayin barazana ta hakika ga tsaro da zaman lafiyar yankin, kuma kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya bai zai iya daukan wani matakin kasa da kasa guda daya na yin Allah-wadai da irin wannan mugun hali lamarin da mayar da kwamitin tsaron ya yi hasarar matsayi da aminci da ake da shi kansa wajen iya wanzar da zaman lafiya da tsaro na duniya.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Siriya ta kammala bayanin ta da cewa: Kasar Siriya ta yi kira ga dukkan kasashen duniya da su sauke nauyin da suka rataya a wuyansu, tare da daukar kwararan matakai na dakatar da kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya suke aikatawa a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da dora wa shugabanninsu alhakin laifuffukan da sojojinsu suke aikatawa da gurfanar da su a gaban kotun kasa da kasa domin hukunta su kan matakan hare-haren wuce gona da iri kan kasashe.

Har ila yau, a cikin ‘yan kwanakin baya-bayan nan rahotonni sun watsa labarin irin matakan wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka kan kasar ta Siriya, inda ta kaddamar da hare-haren zalunci kan yankin Al-Mazzeh da garin Qudusiyya da ke gefen birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Siriya, inda jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi luguden wuta kan al’ummun yankunan biyu tare da lalata musu gine-ginen zama da dukiyoyinsu.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta sanar da matakin yin Allah wadai da harin bama-baman da ‘yan sahayoniyya suka kai a yankunan na Mezzeh da Qudusiyya da suke gefen birnin Damascus, tana mai jaddada cewa, rashin mutunta dokokin kasa da kasa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi na zuwa ne sakamakon gazawar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wajen daukar kwararan matakai na dakile muggan laifukan ‘yan sahayoniyya.

A cikin sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Siriya ta fitar ta bayyana cewa: A wani lamari da ke nuni da munanan kangin da yahudawan sahyoniyawan suka shiga sakamakon gaza cimma manufofinsu na ci gaba da kai hare-hare a kan wasu kasashen yankin, da kuma bude yakin kisan kare dangi a kan al’ummar Falastinu da Lebanon, sojojin mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wasu farmaki ta sama a yammacin ranar Alhamis kan wasu gine-ginen gidajen jama’a a yankin Al-Mezzeh da ke gefen birnin Damascus, da kunshi yankunan gidajen jami’an diflomasiyyar kasashen waje da babban ofisoshin Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Siriya, baya ga wasu hare-hare da suka kai kan wasu gine-gine a yankunan Qudusiya agefen birnin na Damascus. Wannan farmakin da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a gefen birnin Damascus sun kasance kafin wasu sa’o’i na wasu hare-hare da suka kai a kan birnin Homs da gadojin da suke kan kogin Asiy da kuma hanyoyin da ke kan iyakar Siriya da Lebanon a yankin Qusayr.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Siriya ta bayyana cewa:,Ci gaba da kai hare-hare da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a kasar Siriya ya zo ne bayan ‘yan kwanaki da kammala zaman taron hadin gwiwar kasashen Larabawa da Musulunci da aka gudanar a birnin Riyadh na kasar Saudiyya da ya fitar da wani gagarumin tofin Allah tsine kan zaluncin da yahudawan sahayoniyya suke yi da wuce gona da iri kan yankunan Siriya, musamman hare-hare kan fararen hular da ba su da kariya, da lalata gine-ginen zama da ababen more rayuwa, da kuma gargadin sa game da hadarin da ke tattare da wannan tashin hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments