Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Korar sojoijin Faransa daga kasa ta 7 a yammacin Afirka tare bukatar’ macron ya nemi uzurin kasashen’ wanda ni tahir amin zamn karanta.
///…Madalla, Bayan da kasashen Mali da Burkina faso, da Nigerda Ivory Coast suke kori sojojin Faransa daga kasashensu, a yanzun kuma kasar Senegal ta bada sanarwan korar sojojin kasar Faransa daga kasar.
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Mali da kuma korar sojojin kasashen waje, daga cikin har da sojojin kasar Faransa da kuma na Majalisar dinkin duniya daga kasar, daya bayan daya kasashen yankin yammacin Afirka kuma tsoffin kasashen da Faransa tayiwa mulkin mallaka suka suka fara korar sojojin faransa daga kasashensu.
Bayan Burkiya Faso sai Jumhuriyar Niger, sannan Ivory Coast sannan yau kuma Senegal. Wannan yana daga cikin sauye-sauyen da suke faruwa a kasashen yammacin Afirka a cikin yan sheakrun da suka gabata, wanda kuma yake nuna yadda kasashen da aka yiwa mulkin mallaka a wannan yankin, suke kin wadanda suka yi masu mulkin mallaka, hatta bayan sun basu abinda suka kira yenci.
A zahiri dukkan wadannan kasashe, babu ko da guda wacce take da wani cikin gaban a zo a gani, ta ko wani bangare, fiye da shekaru 60 da kasar faransa tace ba basu yencin kai, ba abinda take yi sai kwasar dokokiyoyin wadannan kasashe zuwa kasashensu.
Misali shi ne, an ce kasha 20% na ton 88,200 na sinadarim Uranium da ya shiga kasar faransa a cikin shekaru 10 da suka gabata ya fito daga Jumhuriyar Niger ne. A kasar Mali kasar faransa tana fitar da ton ton na gola-golan zuwa kasar faransa, amma ba zaka taba ganin wata ci gaba a kasar ba.
Kamfanin dillancin labaran Pars today ya nakalto daga tashar talabijin ta Euronews yana cewa ofishin jakadancin kasar Faransa na cewa a ranar Lahadi 9 ga watan Maris, sojojin kasar Faransa sun mika sansanonin sojoji guda biyu da ke hannunsa ga sojojin kasar ta Senegal.
Kafin haka dai a ranar 2 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne kasashen biyu suka kafa kwamitin hadin guiwa na kula da shirin ficewar sojojin faransa daga kasar.
Sai kuma kasar Ivory Coast inda sojojin Faransa suka mika sansanin sojojin kasar tilo a kasar Ivory coast ga sojojin kasar a ranar 20 ga watan Fabrayru. Ministan harkokin wajen kasar Faransa Sepostine Lakunu da tokwaransa na kasar Ivory Coast
Tane Perohimi Watara ne, suka rattaba hannu kan takardun ficewar sojojin kasar faransa, daga kasar.
Kamfanin dillancin labaran Isna na kasar Iran ya bayyana cewa, sojojin kasar Faransa 400 suke zaune a sansanin sojojin kasar. Sannan kwamandan sojojin Ivory Coast ne ya bada sanarwan kawo karshen zaman sojojin kasar Faransa a kasar a wani biki bamusamman da aka gudanar a babban birnin kasar a ranar 19 ga watan Fabrairun shekara ta 2023.
Labarin ya ce a bikinne aka sauke tutar kasar Faransam sannan aka sane shi sai kuma aka daga tutar Burkina faso a inda aka sauko da na faransa.
Amma kafin haka sojojin kasar Faransa sun fice daga kasar Mali ne a ranar 20 ga watan Augustan shekara ta 2022m bayan shekaru 9 da shiga kasar da sunan tabbatar da zaman lafiya.
Komandan rundunar sojojin kasar faransa a Mali, ya bada sanarwan aikin rundunarsa wacce ake kira Barkhane a wannan ranar, inda suka ratsa ta Niger suka kuma fice daga yankin kwata-kwata.
A niger dai sojojin Faransa 1500 ne suke zauna a birnin Yemai, kafin su fice a ranar 22 ga watan Decemban shekara ta 2023. Haka ma kasar Chadi sojojin Faransa sun fice daga wani sansaninsu a birnin Njamena ne, a ranar 30 ga watan Jenerun shekara ta 2024.
Ya zuwa yanzu dai sojojin Faransa sun fice daga mafi yawan kasashen da take zama a cikin, sai kasar Njibuti, inda take da sojojin 1,500 da kum Gabon inda take da sojoji 350.