Sharhin Bayan Labarai: Amurka Ce Ta Horar Da Masu Juyin Mulkin Kasar Siriya

Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan rahoton da ke cewa: Amurka ce ta horar da wata kungiya da ke dauke da makamai

Sharhin bayan labaran namu zai yi magana ne kan rahoton da ke cewa: Amurka ce ta horar da wata kungiya da ke dauke da makamai domin hambarar da gwamnatin Bashar Assad da cikakken bayanin da ya biyo baya, da ni Sunusi Wunti zan jagoranci gabatar muku da shirin kamar haka:-

Jaridar “The Telegraph” ta kasar Birtaniya ta bayyana cewa: Kasar Amurka tana goyon baya tare da horar da wasu gungun ‘yan ta’adda domin shiga harin da ya kai ga kifar da gwamnatin Bashar al-Assad na Siriya.

A cikin wani jawabi da dakarun Amurka na musamman a Siriya suka yi wa gungun mayakan da ke samun goyon bayansu kafin kifar da gwamnatin Siriya, an ce wa mayakan da Birtaniya da Amurka suka horar a cikin sojojin “Kwamandojin Juyin Juya Hali”: Wannan shi ne lokacin ku.

A cewar jaridar, alamar farko da ke nuna cewa; Amurka ta riga ta san batun shirya kai harin, kuma ita ce ta umarci sojojin “kwamandojin Juyin Juya Halin” da suke samun goyon bayanta da su kara yawan dakarunsu da kuma shirya kai harin a cikin Siriya.

Jaridar Telegraph ta nakalto daga Bashar al-Mashhadani, daya daga cikin kwamandojin sojojin juyin juya halin yana cewa: An gaya musu cewa: Komai yana daf da faruwa, kuma lokaci ne da tarihi zai ambace shi, kodai gwamnatin Assad ta fadi ko kuma su zasu fadi, amma ba su fayyace lokacin ba ko kuma a ina, sun ce musu su shirya kawai, kamar yadda gidan talabijin na Al-Mayadeen ta nakalto.

A makonnin da suka gabata a taron manema labarai da dakarun Amurka na musamman suka gudanar a sansanin sojin sama na Al-Tanf, wanda Amurka ke iko da shi a kan iyakar kasar Siriya da Iraki, manyan kwamandojin juyin juya halin sun karu da kananan runduna masu zaman kansu, a cewar Al-Mashhadani.

Al-Mashhadani ya kara da cewa: Adadin dakarun ya karu daga kimanin 800 zuwa 3,000 masu dauke da manyan makamai da Amurka ta karfafa su da su, sannan kowane mayaki ya samu kusan kudi dalar Amurka 400.

Jaridar ta yi nuni da cewa: A yayin da mayakan suka doshi shiyar kudanci a kan hanyarsu ta tafiya birnin Damascus fadar mulkin kasar Siriya, sojojin “kwamandojin juyin juya halin” sun yi gaba a lokacin fitowarsu daga sansanin Al-Tanf, domin hana ragowar ‘yan kungiyar ta’addanci ta “ISIS” yin amfani da faduwar gwamnatin Siriya wajen karbe madafun ikon kasar. wannan shi ne abin da manyan hafsoshin sojin Amurka suka shaidawa kwamandojin ‘yan adawar kasar Siriya.

Wani abin lura a nan shi ne cewa: A wannan lokaci sojojin “kwamandojin juyin juya halin” sun mamaye kusan kashi biyar na yankunan kasar, ciki har da muhimman yankunan da suke arewacin birnin Damascus fadar mulkin kasar ta Siriya.

Jaridar ta yi nuni da cewa: Ba wai kawai Amurka tana sane da harin da Hay’at Tahrir al-Sham ta jagoranta ba ne, har ma tana da sahihin bayanan sirri kan iyakar da harin zai tsaya.

Jaridar ta bayyana cewa da fara kai hari a babban birnin kasar Damascus a ranar 8 ga watan Disamba, dakarun “kwamnadojin juyin juya halin” sun bazu a cikin hamadar gabashin kasar, inda suka kwace iko da manyan hanyoyin kasar, tare da shiga wani bangaren masu dauke da makamai a yankin birnin Dar’a a kudancin Siriya, wanda suka isa birnin  Damascus kafin isar “mayakan Tahrir al-Sham”.

Al-Mashhadani ya bayyana cewa: Sojojin Kwamandojin juyin juya hali da mayakan Hay’at Tahrir al-Sham na da kyakkyawar hadin kai da kuma hadin gwiwa, kuma Amurkawa na gudanar da harkokin sadarwa a tsakanin rundunonin biyu daga sansanin Al-Tanf.

A karshen rahoton jaridar ta “The Telegraph” ta kasar Birtaniya ta yi mamakin yadda aka samu kawance mai karfi tsakanin Amurka da kungiyar ta’addanci irin ta “Hay’at Tahrir al-Sham” ke da alaka da kungiyar Al-Qa’ida a Siriya tun daga kafuwarta har zuwa lokacin da suka raba gari a tsakaninsu a shekara ta 2017.

A gefe guda kuma, Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana hakikanin adadin sojojin Amurka a Siriya tun lokacin wanzuwar gwamnatin Bashar Assad da kuma bayan faduwarta.

Mai magana da yawun Pentagon Patrick Ryder ya bayyana cewa: Adadin sojojin Amurka da ke kasar Siriya a lokacin baya ya kai kimanin sojoji 2,000 ba sojoji 900 ba kamar yadda aka fada a baya.

Ryder ya ce a cikin wani taron manema labarai: “Kamar yadda kuka sani, muna sanar da ku akai-akai cewa kusan sojojin Amurka 900 suna jibge a Siriya.”

Ya kara da cewa: “A yau na samu labarin cewa ainahin adadin sojojin Amurka a Siriya ya kai kimanin sojoji 2,000.”

A cewar mai magana da yawun Pentagon, “Akwai sojojin Amurka 900 a Siriya lokacin da Bashar al-Assad ke kan mulki, kuma an aike da karin dakaru zuwa kasar don inganta aikin da ake yi na fatattakar ‘yan ta’addar ISIS.”

A cewar sanarwar da Pentagon ta fitar a baya, kimanin sojojin Amurka 2,500 ne aka jibge a Iraki, yayin da sojoji kusan 900 ke jibge a Siriya, a wani bangare na yunkurin da ake na yaki da kungiyar ta’addanci ta ISIS, kamar yadda ya yi da’awa.

Amurka dai na amfani da kungiyar ISIS (wacce gungun ‘yan ta’adda ce da kasashen yammacin duniya suka kafa su) a matsayin hujjar zama a Siriya da wawashe dukiyar kasar, yayin da dakarunta suka fi maida hankali a yankunan da ke da arzikin man fetur da iskar gas, kuma a fili suke hakowa da sayar da wadannan dukiya tare da soke kudaden a aljihunsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments