Kasar Faransa ta mika iko na sansanin soja na Contre-Amiral Protet ga kasar Senegel, wanda shi ne sansanin soja na 3 da aka mikawa kasar a bana.
An mika sauran sansanoni biyu da suka hada da Marechal da Sanit-Exupery ne a watan Maris din da ya gabata, Kuma dukkan sansanonin na da mazauni ne a Dakar, babban birnin Senegal.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin Faransa ya fitar, ta ce an tsara mika dukkan wasu sansanonin dake karkarshin ikon Faransa a Senegal a bana, biyo bayan yarjejeniyar da kasashen biyu suka yi.
A ranar 31 ga watan Disamban 2024, shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar a jawabinsa na sabuwar shekara cewa, za a bukaci dakarun Faransa su fara janyewa daga kasar a bana.
A shekarun baya bayan nan dai kasashen Afrika sun yi ta kira da janye dakarun Faransa daga kasashensu.
Shi ma a jawabinsa na sabuwar shekara, shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara, ya gabatar da shirin ficewar dakarun Faransa daga kasarsa.
Tun tuni daga kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar suka raba gari da kasar ta Faransa tare da yanke alakar soji a tsakaninsu, sai kuma kasar Chadi wacce ta bi sahu.