Search
Close this search box.

Sayyid Safiyuudin:  Mayar Da Marttani Akan Shahid Ni’imah Zai Cigaba

Shugaban Majalisar zartarwa ta Hizbullah Sayyid Hashim  Safiyuddin ya bayyana cewa; Mayar da martani akan HKI dangane da shahadar Muhammad Ni’imah Nasir  wanda ya fara

Shugaban Majalisar zartarwa ta Hizbullah Sayyid Hashim  Safiyuddin ya bayyana cewa; Mayar da martani akan HKI dangane da shahadar Muhammad Ni’imah Nasir  wanda ya fara tun jiya, zai cigaba  cikin karfi.”

Safiyuudin ya fada a yau Alhamis cewa:Tun jiya Laraba ne aka fara mayar da martani mai karfi akn kisan gillar da HKI ta yi wa Shahid Muhammad Ni’imah, kuma ana cigaba da kai wa, yana mai kara da cewa: “Wajibi ne abokan gaba HKI su fahimci cewa; kai wa kwamandoji irin wadannan hari, zai sa su sami saukin shiga cikin kudancin Lebanon.

Safiyuddin wanda yake jawabi a wurin jana’izar Shahid Ni’imah a unguwar Dhahiyah a birnin Beirut, ya kuma kara da cewa; A karkashin gwgawarmayarmu, tuta bat a faduwa kasa, kuma ba a sami rauni a fagen daga, don haka a duk lokacin da wani kwamanda ya yi shahada, wani zai maye gurbinsa.

Shugaban Majalisar zartarwar ta kungiyar Hizbullah, ya fada wa HKi cewa; Kisan gillar da ta yi wa kwamanda Ni’imah, bai ba ta wani fifiko ba ko nasara, tare da cewa; sojojin HKI suna fuskantar cin kasa mai tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments