Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Al’ummar musulmi suna fuskantar manyan hatsari guda biyu, da su ka hada laifukan da HKI take tafkawa a Gaza, da kuma kokarin shafe hakkokin falasdinawa baki daya.
Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma tabo batun keta tsagaita wutar yaki da HKI take yi a kasar Lebanon yana mai kara da cewa, keta hurumin kasar Lebanon da ‘yan sahayoniyar suke yi, ya isa har birnin Beirut.
Akan kasar Syria ma, jagoran na kungiyar Ansarullah na Yemen ya yi ishara da hare-haren da ‘yan sahayoniya su ka kai a cikin biranen Damascus, Hums da Dar’a.
Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce,abokan gaba sun mayar da keta hurumin kasashen al’umma abinda za su rika yi kodayaushe. Haka nan kuma ya ce ko kadan bai kamata a mayar da kisan da ake yi wa Falasdinawa ya zama wani abu da ake gani yana faruwa a kowace rana ba.
Sayyid Abdulmalik ya yi kira da a sake dawo da fafutukar da ake yi a duniya baki daya, ta nuna kin amincewa da abinda yake faruwa a Gaza ba.