Iran ta jaddada shirinta na fadada huldar soji da kasar Saudiyya a wani bangare na batutuwan da ziyarar ministan tsaron kasar Saudiyya Tehran ta kunsa.
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Bagheri ya shaidawa Yarima Khalid bin Salman a Tehran a wannan Alhamis cewa “Kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojinsu za ta kawo yanke kauna ga makiyanmu da kuma sanya farin ciki ga abokanmu da sauran musulmi”.
Bagheri ya godewa Saudiyya a kan halartarta a matsayin mai sa ido a babban atisayen sojojin ruwa na tekun Indiya (IONS), wanda aka fi sani da IMEX 2024.
Iran, Rasha, da Oman ne suka gudanar da atisayen a tekun Indiya, tare da halartar tawagogin masu sa ido daga kasashe da dama da suka hada da Saudiyya, Indiya, Thailand, Pakistan, Qatar, da Bangladesh.
Yarima Khalid ya bayyana godiyarsa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma babban hafsan sojin kasar bisa kyakkyawar tarba da suka yi masa tare da tawagarsa a birnin Tehran, yana mai cewa: “karamcin da kuk a yi mana yana nuna kyakkyawar alaka mai karfi da ke tsakaninmu”.