Ma’aikatar kiwon lafiya a kasar Saudia ta kaddamarda wata manhaja don kula da lafiyan mahajjata a hajjin bana, wanda aka tarjamata zuwa harsuna 8 a duniya.
Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto kamfanin dillancin labaran Saudi Press Agency (SPA) na fadar haka a yau Jumma’a. Ya kuma kara da cewa harsunan da ake samun manhajar a ciki suna hada da Arabiyya, Inglishi, Faransaci, Urdu, Farisanci, Indonesia, Malay da kuma Turkanci.
Manufar wannan manhajar ita ce bada shawara ga mahajjata kan yadda zasu kula da lafiyarsu a cikin wannan lokacinda Hajji na bana, wanda yake zuwa tare da zafi sosai.
Da farko manhajan ya bukaci mahajjata su yi amfani da laima don rage zafin da ke fadawa a kansu. Sannan su tabbatar da cewa sun yi alluran riga kifan da yakamata su yi tun suna kasashensu, wadanda suka hada da cutar Corona ko covid 19, shan inna, cutar shawara, da malariya, da sauransu. Wannan ya danganci daga kasar da mutum ya fito. Ana samun manhajan a yanar gizo ko a kan wayoyi da sauransu a kan adireshin