Saudiya Ta Bukaci A Kafa Kasar Falasdinu Don Kawo Karshen Rigima A Gabas Ta Tsakiya

Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya. Shafin yanar gizo na

Gwamnatin kasar Saudiya ta bukaci a amince da samuwar kasar Falasdinu mai zamanta ne kawai hanyar warware rikicin gabas ta tsakiya.

Shafin yanar gizo na labarai Arabnews na kasar Saudiya ya nakalto majiyar Saudia na fadar haka a MDD a jiya Jumma’a. Ta kuma kara da cewa Falasdinawa ba zasu taba amincewa a koresu daga kasarsu ba kamar yadda wasu yahudawa da magoya bayansu suke so.

Labarin ya kara da cewa wannan bukatar na zuwa ne a dai-dai kasashen ta    Saudia da Faransa suke kokarin gudanar da gagarumin Taro a cikin watan Yuni mai zuwa don bunkasa wannan ra’ayin ta kafa kasashe biyu.

Wannan ra’ayin yana kara samun goyon baya a wannan makon musamman bayan da HKI ta kara yawan kissan da takewa Falasdinawa a Gaza, wadanda suka ki barin kasarsu zuwa ko ina a duniya.

Manal Radwan daga ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiya wacce kuma take daga cikin wadanda suke shirin taron na NewYork ta fadawa majalisar kan cewa matsalolin rikicin falasdinawa da HKI suna da dama amma mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne rashin amincewa da samuwar juna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments