Afrika ta kudu ta karyata ikirarin da shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kan cewa kasar ta aikata kisan kiyashi kan manoma fafaren fata a Afrika ta Kudun.
Ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu, Senzo Mchunu, ya yi fatali da ikirarin naTrump, yana mai cewa bai da tushe balle makama, in ji jaridar Daily Maverick ta Afirka ta Kudu.
Ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu ya fada jiya Juma’a cewa babu wani abu da ya yi kama da hakan a game da ikirarin da Trump na kisan kiyahsin fararen fata a yayin ganawarsa da shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.
Trump dai ya nuna wani faifan bidiyo yayin ganawarsa da takwaransa na Afrika ta Kudu, inda har ma ya nuna hotunan wasu gawawaki a gefen titi, wadanda ya danganta da manoma farar fata da aka kashe.
Mista Mchunu ya ce karyar da Mista Trump ya yi na daga cikin “labarinsa na kisan kare dangi” – yana mai nuni da zarge-zargen mara tushe da shugaban Amurka ya yi na cewa akwai wani kamfen da ya bazu a Afirka ta Kudu na kashe fararen fata tare da kwace musu gonakinsu, wanda ya ce ya yi daidai da kisan kare dangi.
Awani labarin kuma wasu kafofin yada labarai sun ce wasu hotunan da Trump ya nuna basu da alaka da wani abu da ya faru kamar haka Afrika ta Kudu.
Kamfanin dinacin labaren Reuters ya ce wani hoton tsohon labarinsu ne na wani lamari da ya faru a RDC.