Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sallami ma’aikata da dama a majalisar tsaron kasar Amuka saboda gazawarsu wajen magance wasu al-amuran tsaro da siyasa a kasar.
Tashar talabijin Ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Rauters yana cewa ma’aikatan maimakon su magance al-amuran tsaro da suka shafi tsaron kasa, sai sun zauna suna jiran abinda shugaban zai fada don su yi aiki a kansa.
Labarin ya kara da cewa shugaban ya dauki wannan matakin ne don ya mika wasu ayyukansu ga Pentagon da FBI da wasu ma’aikatun tsaro don magance wasu matsaloli masu muhimmanci a cikin sauri.