Ofishin yada labaran Gaza ya bayar da rahoton mutuwar Falastinawa 299 da suka fada cikin mawuyacin hali na rashin abinci mai gina jiki, da karancin kayan masarufi da magunguna.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar talabijin ta Aljazeera na cewa, taimakon jin kai na cikin hadarin rubewa saboda haramcin da gwamnatin sahyoniyawan ta kakabawa na shiga Gaza a yayin da al’ummar zirin ke fama da yunwa.
Ofishin yada labarai na Gaza ya kara da cewa: Gwamnatin Sahayoniya ta yi ikirarin cewa ta ba da izinin shigar da ayarin motocin agaji yayin da manyan motoci 300 ne kawai suka shiga zirin Gaza.
Gwamnatin mamayar ta tilasta wa ayarin motocin agaji bin hanyoyin da ke da hatsarin gaske.
Har ila yau gwamnatin na kai hari kan kungiyoyin ceto, kuma a baya-bayan nan masu ceto shida sun yi shahada a bakin aikinsu, in ji rahoton.
Wannan lamarin ya haifar da mummunan sakamako, ciki har da mutuwar Falasdinawa 58 daga rashin abinci mai gina jiki da kuma wasu 242 saboda karancin magunguna da abinci.
Sojojin Isra’ila sun sake kai hare-hare a Gaza a ranar 18 ga Maris, inda suka kashe dubban Falasdinawa, tare da raunata wasu da dama, bayan da suka rusa yarjejeniyar tsagaita bude wuta na tsawon watanni 2 da kungiyar Hamas ta Falasdinu da kuma yarjejeniyar musayar fursunonin Isra’ila da Falasdinawa da aka sace.
Akalla Falasdinawa 53,822 aka kashe, akasari mata da yara, da kuma wasu mutane 122,382 da suka jikkata a mummunan harin da sojojin Isra’ila suka kai a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.