Guterres: MDD Ba Za Ta Shiga Duk Wani Shiri Da Ba Zai Girmama Dokokin Kasa Da Kasa Ba A Gaza

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani tsari da ba zai girmama dokokin kasa da kasa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa; MDD ba za ta shiga cikin duk wani tsari da ba zai girmama dokokin kasa da kasa ba a Gaza.

Bayanin nasa dai ya zo ne a matsayin mayar da martani akan maganar da ta fito daga HKI na cewa tana aiki tare da Amurka domin raba kayan agaji a Gaza.

Babban magatakardar MDD ya kuma kara da cewa; kaso 80% na yankin Gaza, ko dai yana karashin mamayar Isra’ila da kuma wanda aka bai wa mazaunansa umarnin su fice daga cikinsa.”

Antonio Guterres ya yi gargadin cewa matukar ba a bude iyakoki ba, aka kuma shigar da kayan agaji, to mutanen Gaza za su rasa rayukansu.”

Babban magatakardar MDD ya tunawa HKI cewa, a matsayinta na ‘yar mamaya, wajibi ne ta mutunta fararen hula da kare karamarsu kamar yadda dokokin kasa da kasa su ka tanada.”

Haka nan kuma ya yi kira da a dakatar da yaki a cikin gaggawa,kuma wajibi ne a yunkura a yanzu domin a kowace rana ana kara samun wadanda suke rasa rayukansu da kuma jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments