Kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu ta yi kakkausar suka kan kalaman baya-bayan nan da dan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican Randy Fine ya yi, wanda ya yi kira da a kai wa zirin Gaza hari da makamin Nukiliya.
Kungiyar Hamas, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana kalaman dan ‘majalisar a matsayin “laifuffuka” da kuma nuna wariyar launin fata na wasu sassan Amurka.
Kungiyar ta bukaci hukumomin Amurka da na majalisar dokokin kasar da su fito fili su yi Allah-wadai da irin wadannan kalamai.
Hamas ta jaddada cewa furucin dan majalisar Republican na nuni ne karara ta keta dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Geneva, kuma yana nufin tunzura kai tsaye don amfani da makaman kare dangi kan fararen hula fiye da miliyan biyu a Gaza.
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta bayar da sammacin kame a watan Nuwamban da ya gabata ga firaministan Isra’ila Netanyahu da tsohon ministan harkokin soji Yoav Gallant, bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Gaza.
Har ila yau Isra’ila na fuskantar shari’ar kisan kiyashi a kotun kasa da kasa kan yakin da ta yi kan yankin gabar tekun da ta yi wa kawanya.