Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; An sami shahidai 3 da aka kai su asibitin a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata.
Shi kuwa ofishin gwamnati dake Gaza ya sanar da cewa, daga tsagaita wutar yaki zuwa wannan lokacin, sau 591 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta keta wutar yaki.
Ofishin gwamnatin a yankin Gaza ya yi tir da hare-haren na Haramtacciyar Kasar Isra’ila, tare da yin kira ga kasashen duniya da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya masu keta dokokin kasa da kasa.
Kididdiga ta bayyana cewa daga tsagaita wutar yaki a ranar 11 ga watan Oktoba 2025, adadin Falasdinawa da su ka yi shahada sun kai 356,yayin da wadanda su ka jikkata sun kai 908.
Haka nan kuma a wannan tsakanin an fito da gawawwakin Shahidai 607 daga karkashin baraguzai.