Kamfanin dillancin labarun Qatar ( Qana) ya sanar da cewa, sarkin kasar Sheikh Tamim Bin Hamad ali-Sani ya baro Doha akan hanyarsa ta zuwa Tehran.
Majiyar ta kara da cewa, sarkin na Qatar zai zo da tawagar tattalin arziki da kuma siyasa. Baya ga batun tattalin arziki, bangarorin biyu za su tattauna batutuwan da su ka shafi Gaza da kuma Amurka, kamar yadda kamfanin dilllancin labaun Mehr ya nakalto.
Jakadan Jamhuriyar musulunci ta Iran a Qatar, ya saanr da cewa ziyarar da sarkin na Qatar zai kawo Tehran tana a karkashin kokarin bunkasa alakar kasarsa da Iran.