Sama da mutane 1,560 ne sukayi shahada tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki Gaza

Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar

Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza.

Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan jiya ya zarce 1,560 a cewar jami’an kiwon lafiya.

A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar yau Asabar, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan.

An kashe mutane 50,933 tare da raunata 116,045 tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, in ji ma’aikatar a alkalumman data sabunta.

A cewar hukumar ‘yan gudun hijira ta Falasdinawa UNRWA, kimanin Falasdinawa 400,000 ne aka tilastawa barin muhallansu a fadin Gaza tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta fara aiki a watan Janairu ta ruguje kusan wata guda da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments