Sama da mutane 1,000 suka mutu a rikicin Siriya

Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke

Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) da kungiyoyin dake da alaka da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000 a cikin kwanaki biyu kacal.

Wannan tashin hankalin, ya fi shafar yankin yammacin Syria, wanda ya kara ta’azzara halin da ake ciki.

A baya dai kungiyar ta bayar da rahoton cewa, an kashe akalla mutane 237 da suka hada da 142 wadanda ba mayakan ba ne a yankin gabar ruwan kasar ta Syria, tun bayan fara kazamin fada a ranar Alhamis din da ta gabata.

Wadannan al’amura dai na nuni da karuwar tashe-tashen hankula, mafi muni da aka gani tun bayan faduwar gwamnatin da ta shude a watan Disambar da ya gabata.

Shugaban Syria Abu Mohammed al-Jolani ya yi kira da a samar da zaman lafiya da hadin kan kasa bayan tashe tashen hankula a kasar a baya-bayan nan, yana mai jaddada cewa abubuwan da ke faruwa na daga cikin kalubalen da ake iya fuskanta.

Wannan sabon lamari na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun HTC suka kara kaimi wajen murkushe ragowar tsoffin sojojin Syria a lardunan Latakia, Tartus da Hama.

Ana gwabza fada ne a yankin gabar tekun arewa maso yammacin kasar, inda galibin al’ummar kasar ke da ‘yan tsiraru ‘yan Alawiyya, wanda shi ma tsohon shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya fito.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments