Shugaban kasar Namibia dake kan gado Nangolo Mbumba ne ya sanar a yau Lahadi cewa, jagoran samun ‘yacin kasar Sam Nujoma ya rasu a jiya Asabar da dare, bayan da aka kwantar da shi a wani asibitin babban birnin kasar Windhoek.
Sanarwar da shugaban kasar ta Namibia mai ci a yanzu, ya fitar ya bayyana mutuwar Nujoma da cewa; ginshikin da aka kafa kasar akansa ya girgiza.
Sam Nujoma ya jagoranci fadan sama wa kasar ta Namibia ‘yanci daga mulkin nuna wariyar launin fata na Afirka ta kudu, a shekarar 1990, sannan kuma ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 15.
A lokacin da yake a raye, al’ummar kasar ta Namibia suna girmama shi matuka a matsayin wanda ya jagoranci fadan samun ‘yanci sannan kuma ya dora kasar akan turbar demokradiyya.
A yayin gwagwarmayarsa ta nema wa kasar ‘yanci, Nujoma ya yi shekaru 30 yana gudun hijira. Kasar dai ta sami ‘yanci ne daga mulkin mallakar tsarin Wariya na Afirka ta Kudu a 1989, bayan da a baya ta kasance a karkashin mulkin mallakar jamus. Majalisar dokokin kasar ta zabe shi a matsayin shugaban kasa a 1990.
Nujoma ya kasance a sahu daya da jagororin da su ka yi fafutukar samun ‘yanci a nahiyar Afirka da su ka hada Nelson Mandela na Afirka Ta Kudu, Robert Mugabe na Zimbabwe, Kenneth Kaunda na Zambia, Julius Nyerer na Tanzania da Samora Machel na Mozambique.
Kungiyar neman ‘yanci ta SWAPO wacce Nujoma ya jagoranta ta dauki shekaru 20 tana fada da makamai, wacce kuma ta sami cikakken goyon baya a duniya daga ciki har da MDD.