Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Karbi Bakwancin Takwaransa Na Iraki

Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya karbi bakwancin takwaransa na kasar Iraki a birnin Tehran Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali

Babban sakataren majalisar kolin tsaron kasar Iran ya karbi bakwancin takwaransa na kasar Iraki a birnin Tehran

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya karbi bakwancin mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji.

A yau litinin ne mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro, Qasim al-Araji, ya iso birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, inda yake jagorantar wata babbar tawaga ta tsaro.

Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya gana da mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro Qasim al-Araji, inda suka tattauna batutuwa da dama musamman kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da muhimman mu’amalar da ke tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted