Shuwagabannin kungiyar kasashen raya tattalin arziki da kuma tsaron kasashen Afrika da kudu ta ce zasu ci gaba da wanzar da sojojinsu a kasar Congo duk tare da sauye-sauyen da kungiyar yan tawaye na M23 suka yi a yankin arewacin KIVU.
Shafin yanar gizo na Labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa shuwagabannin kungiyar sun bada wannan sanarwan ne bayan wani taron gaggawa da suka gudanar a kasar Zibabwe a ranar Jumma’an da ta gabata.
Shugaban kungiyar na riko-riko kuma shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya yim kira ga kungiyar ta kasance mai nuna karfi da da kuma juriya kan abubuwanda da ke faruwa a arewacin congo.
Sojojin tabbatar da zaman lafiya na kungiyar a cikin makonnin da suka gabata sun fuskanci koma baya a hannun sojojin M23, inda suka kashe sojojin kungiyar kimani dozen guda daga kasashen na SADC.
Affirka ta kudu, Malawi, da Tanzania sun rasa sojoji a dai dai lokacinda sojojin M23 suka shiga birnin Goma babban birnin. A halin yanzu dai shugaba Tsetsekedi ya fara tattara sojojin kasar don kare birnin Kinshasa babban birnin kasar ta Congo.