Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya
Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar da Siriya daga cikin sahun masu fada da makirce-makircen yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ta hanyar kulla kyakkyawar alaka da su, da janyewa daga duk hakkokin kasar Siriya da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta mamaye na Siriya a baya-bayan nan.
Manufar samar da sabuwar gwamnatin masu da’awar jihadi, kamar yadda aka sani, ita ce tabbatar da tsaron babban sansanin Amurka mafi girma a yanking abas ta tsakiya, wato “haramtacciyar kasar Isra’ila.”