Saboda Rikicin Kasar Sudan Ta Kudu Shugaba Musaveni Ya Isa Birnin Juba

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya isa birnin Juba na kasar Sudan ta kudu a yau Juma’a, a kokarin lalubo hanyar warware dambaruwar siyasar da

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya isa birnin Juba na kasar Sudan ta kudu a yau Juma’a, a kokarin lalubo hanyar warware dambaruwar siyasar da kasar take ciki da hana barkewar sabon yakin basasa.

 Jim kadan bayan yi wa mataimakin shugaban kasar Riek Machar daurin talala a gidansa ne kasar ta shiga zaman dar-dar da fargabar sake komawa cikin yakin basasa.

Da akwai kawance a tsakanin shugabannin kasashen Uganda Mosaveni da kuma Silva Kiir na kasar Sudan Ta Kudu.  Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai kasar ta Uganda ta aike da sojoji masu yawa zuwa kasar ta Sudan ta Kudu, domin bayar da kariya ga gwamnatin Juba.

Gwamnatin Salva Kir tana zargin Machar da cewa yana rura wutar wani sabon yaki a cikin kasar. A ranar Laraba ta makon da ya shude ne dai aka yi wa mataimakin shugaban kasar daurin talala a gidansa saboda fadan da ake yi a yankin Upper Nile tsakanin sojojin gwamnati da kuma masu dauke da makamai na rundunar “White Army”.

Tawagar tarayyar Afirkan da ta isa birnin Juba  wacce ta kunshi majalisar dattijan nahiyar Afirka,  a kokarin shawo kan  rikicin da kasar ta fada.

Tarayyar Afirkan ta fara kokarin shiga tsakani ne, bayan daurin talala da aka yi wa mataimakin shugaban kasa Riek Machar a gidansa,lamarin da ya sake jefa kasar cikin zaman dar-dar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments