A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Rwanda ya fitar, ta zargi kasar ta Belgium da tsoma baki a harkokin cikin gidanta.
Bugu da kari, sanarwar ta bai wa jakadan kasar Belgium a Kigali sa’o’i 48 da ya fice ya bar kasar.
Sanarwar ta kunshi cewa: A kodayaushe kasar Belgium tana kaskantar da Rwanda,tun kafin rikicin kasar DRC, da kuma bayansa, alhali kasar ta Belgium tana da dogon tarihi ta keta, musamman akan Rwanda.”
Kasar Belgium dai ta dakatar da taimakon da take bai wa Rwanda saboda rawar da Kigali take takawa a rikicin kasar DRC.
A wani jawabi da shugaban kasar ta Rwanda ya yi a ranar Lahadi ya bayyana cewa; Kasarsa za ta kare manufofinta da hana kasashen waje yi ma ta katsalandan a harkokin cikin gidanta. Haka nan kuma ya zargi Belgium din da aikata laifuka a tsawon lokacin mulkin mallakar da ta yi wa kasarsa, yana mai kara da cewa za su ci gaba da fada da sabon salon mulkin mallaka.
Kasar ta Rwanda tana fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya saboda goyon bayan da take bai wa ‘yan tawayen kungiyar M23 da su ka kwace iko da manyan biranen Bukavu da Goma da suke a gabashin kasar DRC. Ana zargin cewa kasar ta Rwanda ta aike da sojoji 4000 da suke yaki a tare da ‘yan tawayen.