Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango

Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon

Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin.

Zaftarewar ƙasa ta faru ne a wurin Kalandu da ke cikin ma’adinan Mulundu kusa da Kolwezi, wani wuri da kamfanin Bajiklem ke gudanar da shi a hukumance.

Ministan harkokin cikin gida na lardin, Rui Kawumba Mayondi, ya ce “masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan wurin duk da haramcin da aka sanya saboda ruwan sama mai ƙarfi da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa,” ya ƙara da cewa “hawa da suka yi cikin gaggawa ya sa gadar da suka gina a kan wani rami da ambaliyar ruwa ta mamaye ta ruguje.”

Jami’in ya bayyana cewa zuwa yanzu ƙungiyoyin ceto sun gano gawawwaki 32 daga cikin tarkacen, kuma ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments