Kwamandan sojan kasa na Rudnunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgerdiya Janar Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin kasar a shirye suke su mayar da martani akan duk wata barazana daga abokan gaba saboda suna da zaratan mayaka da kuma sabbin makamai.”
Har ila yau Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin za kuma su yi amfani da kwarewar da tsofaffin sojoji suke da ita, haka nan kuwa darussan da su ka koya daga kallafaffen yakin kwanaki 12 da HKI.
Janar Jahanshahi ya kuma ce; A wannan lokacin kwarewar da sojojin kasa na Iran suke da su, ta kai koli saboda wararrun masana da kuma amfani da fannoni mabanbanta na ilimomi, musamman kirkirarriyar Fasaha.”
A dalilin hakan, sojojin suna cikin Shirin mayar wa da abokan gaba martani idan su ka kawo wani hari.