A kalla tsoffin sojojin rundunar “Gulani” ta HKI 150 ne su ka rattaba hannu akan takardar yin kira da a dawo da fursunoni gida daga Gaza.
Ita dai rundunar “Gulani” ce mafi karf a tsakanin rudunonin sojan HKI,kuma tun da aka kafa ta, ta shiga dukkanin yake-yaken da HKI ta yi.
Wadanda su ka rattaba hannu akan wasikar sun bayyana goyon bayansu ga wasikar da sojan sama su ka rubuta a ranar 9 ga watan Aprilu da ake ciki,ko da kuwa sakamakon hakan shi ne kawo karshen yaki.
A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,dubban sojojin HKI sun rattaba hannu akan wasika wacce take yin kira da a kawo karshen yakin Gaza da kuma dawo da fursunonin da suke can.
A ranar juma’ar da ta gabata kafafen watsa labaru HKI sun ambaci cewa, da akwai sojojin bayan fage 1000 da su ka rattaba hannu akan wasika, da kuma tsofaffin sojojin soja a tsakaninsu da akwai wadanda suna kan ganiyar aikinsu.
Bayan wannan ne kuma sojojin dake kula da motocin yaki da tankoki su 15,25 su ka bi bayansu, sai kuma wasu tsoffin sojojin sama Jannati ,haka nan kuma sojan ruwa da likitocin soja 100. A cikin kwanaki kadan da su ka gabata ma dai wasu jami’an daga cikin tsoffin ma’aikatan kungiyar leken asirin soja sun shiga cikin masu rubuta wasikar.