Ronaldo Ya Zama Biloniya Na Farko Tsakanin Yan Kwallon Kafa A Duniya.

Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta

Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi.

Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai  dalar Amurka miliya 18.

Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da ake biya fam miliyan 177 duk shekara.

Ƙwantiraginsa zai kare a karshen Yunin 2025, amma ya tsawaitata zuwa kaka biyu kan dalar Amurka miliyan 400.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted