Tsohon wakilin Amurka na musamman a kan lamurran Iran Robert Malley, ya caccaki gwamnatin Donald Trump game da kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, lamarin da ya ce babban kure ne wanda kuma zai haifar da mummunan sakamako.
Robert Malley ya ce; ina tsammanin zabi na soja ba daidai ba ne bisa kowane irin dalili. Ba ya kula da matsalar da ke tattare da hakan sosai. Lamarin da zai haifar da rashin tabbas da sakamakon da ba za a iya tsammaninsa ba, ba kawai a cikin kwanaki masu zuwa, ko makonni ba, har ma watanni ko shekaru masu zuwa.
Don haka ina tsammanin cewa wannan shi ne zabi na kuskure da Trump ya dauka, in ji Robert Malley a wata hira da tashar labarai ta NBC ta Amurka.
Ya kuma kara da cewa, mutanen da suke tunanin cewa harin da Isra’ila da Amurka suka kaiwa zai haifar da tayar da kayar baya a cikin gida a Iran, shima wani kuren lissafi ne, saboda hare-haren da gwamnatocin kasashen waje ke kai wa ba wai kawai kan cibiyoyin nukiliyar Iran ba ne, har da asibitoci, da kuma kashe fararen hula.
Ya ce wasu abokansa Amurkawa ‘yan asalin kasar Iran gaya masa cewa, Iraniyawa suna kara samun hadin kai da kishin kasa a duk lokacin da aka kaiwa kasarsu farmaki.