Sakataren majalisar koli na tsaron kasar Iran Janar Mohsen Rezaei ya bayyana cewa duk wani matakin da makiya suka dauka, iran zata maida martani, sannan kasar tana shirin yaki na gaba.
Kamfanin dillancin labaran Mehranews na kasar Iran ya nakalto Janar Rezaei yana fadar haka a jiya Laraba, ya kuma kara da cewa, a halin yanzu Iran ta kammala shirin yaki nag aba. Idan Amurka ta zabi hanyar Diblomasiyya a shirye take, idan kuma ta zabi yaki a shirye take.
Janar Mohsen Rezaei ya kara da cewa, Iran a yake yaken da suka gabata bata yi amfani da dukkan karfin makaman da take da su ba, don haka tana da karfi wanda har yanzun makiya basu taba gani ba.
A wani bangaren na maganarsa Rezaie ya ce, ci gaba da wannan halin da ake ciki a halin yanzu baa bin amincewa bane, saboda ko a halin yanzu aka tsaya, kasuwannin man ba zasu koma yanda suke ba nan da shekaru 3 masu zuwa. Idan kuma abin ya kara lalacewa lamarin zai kara muni.
Daga karshe ya fadwa kasashen Larabawa kan cewa, Amurka ta kasa kare sansanoninta a kasashensu, don haka kada su yi tsammanin cewa zata karesu.