1.
Shin kun san cewa Netanyahu ya yanke shawarar yin wasa da hankalin Yammacin duniya don ya ci gaba da mulki? Ta yaya? Ta hanyar saka musu kiyayya da Musulunci! Bari mu yi dubi kan batun.
2.
Maganar ita ce cewa wani firayim minista dan daba, wanda ke da mummunan tarihi a Gaza, ya zama “mai kare Yammacin duniya”!
3.
Saboda dalilai uku. Na farko: Yaudara.
4.
Har zuwa baya-bayan nan Isra’ila tana kiran kanta da daular dimokuradiyya daya tilo a Gabas ta Tsakiya, don yaudarar zukatan al’ummomin Yammacin duniya!
5.
Amma a yau bayan da Yammacin duniya suka shaida kisan gilla a Gaza da idanunsu, da wuya Turawan Yamma su yarda da hakan, ko ya kuke gani? Saboda a yanzu lamurra suna sauya alkibla!
6.
Yanzu maimakon kare Isra’ila, ya koma yana sukar Musulmi. Maimakon ya ce Tsaronmu yana cikin Hadari kamar yadda yake yi a baya, yanzu ya koma yana cewa, musulmi suna kiyayya da turawa, kuma hakan shi ne babbar barazana ga Yammacin duniya!
7.
Na Biyu: Amfani da Rauni na masu ra’ayin rikau
8.
Gungun masu ra’ayin rikau a Amurka da Turai suna neman hujja don zartar da manufofinsu na nuna wariya.
9. Ta hanyar amincewa da tallafa wa wadannan kungiyoyi, Netanyahu ya ba su halasci, kuma a madadin haka ya sayi goyon bayansu a siyasance don cimma burinsa na siyasa a Turai.
10.
Wannan wani shiri ne mai manufa guda daya: wato mayar da Yamma zuwa mulkin wariya ta hanyar masu tsattsauran ra’ayi, domin tseratar da gwamnatin wariya ta sahyuniya a Falasdinu.
11.
Na Uku: Saka Matsorata a cikin firgici da damuwa
12.
A bisa bayanan da ke cikin takardun sirri da aka fallasa, Isra’ila ta tabbatar da cewa za ta iya sauya ra’ayin jama’a ne kawai ta hanyar Saka tsoro a cikin zukata, amma ba ta hanyar fadin gaskiya ba.
13.
Saboda haka maimakon samun nasarar karbuwa a zukata, suna neman kirkiro wani tsoro na bogi domin saka matsorata a cikin damuwa.
14
Don haka Netanyahu da tawagarsa sun mayar da batun kyamar Musulunci a matsayin makami mafi muhimmanci don sarrafa tunanin ‘yan siyasa, manyan mutane, da kuma sauran mutane.
15
Da nufin nuna Musulmi a matsayin masu cin zarafi, domin su yi amfani da hakan wajen karfafa turawa masu tsattsauran ra’ayi , da kuma yada ta’addanci!
16
Ga alama Netanyahu ya nuna kamar bai damu da sauyin da aka samu ba, dangane da yadda ake Kallon Isra’ila a halin yanzu a cikin kasashen turi, inda a baya da dama suke kallonta a matsayin aboki, yanzu kuma Babbar musiba. Abin da ya fi muhimmanci wurin Netanyahu kawai shi ne sakamakon da shirinsa zai haifar !
17
Amma tambaya mafi mahimmanci ita ce: Shin al’ummomin Yammacin duniya da suka shaida faɗuwar azzalumai da suka mayar da kansu iyayen giji, za su faɗa a cikin tarkon wannan makiri da ke boye fuskarsa ta gaskiya, ko kuwa a wannan karon za su canza hanya?