Nuna Karfi

Shirin Nuna Karfi ya yi nazari kan dalilan da Iran ke bayarwa wajen karfafa matakan mayar da martani ga Amurka, da tasirin wannan dabarar kan

Share

Hoton shirin Nuna Karfi kan martanin Iran ga Amurka da tasirin rikicin kan tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.
  1. Shin an kai Iran a bango ne har ta dauki matakin martani a kan Amurka?
  2. Dan majalisar dokokin Iran Amir Hayat-Moghaddam ya bayyana mahangarsa kan wannan batu mai sarkakiya.
  3. Ya ce: “Hanya daya tilo da za a iya hana Amurka aikata laifi ita ce Iran ta zama mai karfi na mayar da martani.”
  4. Wannan furuci, wanda masana da masu sharhi da yawa na Iran suke maimaita shi a yau, suna cewa ba batun barazana ba ne, suna ganin abu ne da ya kamata, a lokaci guda kuma tare da tafiya da diflomasiyya.
  5. Amma me ya sa Iraniyawa suka dauki matakin harba wasu makamai a cikin teku?
  6. Amsar hakan bisa ga yadda suka fayyace lamarin tana a kan matakai uku.
  7. Na farko: Wannan shi ne harshen da Amurka ta fi fahimta.
  8. Rashin aiwatar da yarjejeniya, da kuma kai hari kan gabar tekun kudancin Iran, a wannan karon hakan ya zo ne bayan sanya hannu kan Yarjejeniyar fahimtar juna ta ranar 17 ga Yuni, inda kuma abin da ya biyo bayan hakan shi ne salwantar rayukan fararen hula kimanin 30.
  9. A mahangar Tehran, Washington ba ta aiwatar da abin da aka cimma matsaya a kansa a cikin yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu ba.
  10. Wannan yasa a yanzu Iraniyawa sun dauki matsaya kan cewa, a duk lokacin da daya bangaren yarjejeniya bai yi aiki da ita ba, su ma za su jingine ta a gefe.
  11. Na biyu, bukatar hana rikici daidai gwargwado.
  12. Abubuwan da suka faru sun tabbatar wa sojojin Iran da ‘yan siyasar kasar cewa, hana barkewar rikici ba zai tabbata ba sai idan babu barazana ta tsaro a cikin yankin.
  13. Amurka tana tafiyar da yakin ne daga nesa, to amma kuma sansanoninta a gabas ta tsakiya sun zama abin kaiwa hari cikin sauki.
  14. Da alama dai Tehran a yanzu tana son yin amfani da salon yaki ne na mayar da martani daidai da hari a kanta, wanda hakan ke nufin yakin zai fita daga iyakokinsa.
  15. Na uku, dole ne asarar bangarorin biyu ta zama iri daya.
  16. Iran ta yi imanin cewa, tsaron yankin gabas ta tsakiya da ikon sarrafa hanyoyin fitar da makamashi suna a karkashin ikon ‘yan siyasa a Fadar White House ne.
  17. Saboda haka, sabuwar dabarar fita daga wannan tarko a bisa mahangar Iran, ita ce karfafa ikonta a mashigar ruwan yankin, wanda shi ne yake da babban tasiri a kan dukkanin lamurran yankin Tekun Farisa.
  18. A kan wannan batu Tehran ba ta yi sassauci ko lallashin Amurka ba. Wanda idan lamarin ya ci gaba da kasancewa a haka a wannan mashiga, kenan yana nufin kawo karshen tasirin Amurka a gabas ta tsakiya.

19.
Tambaya a nan ita ce: Shin Washington a shirye take ta biya kudin fito ga kasar da ta dauka a matsayin babbar abokiyar gaba?