KAUDA KAI DAGA TARON ARBAEEN

Me ya sa babban taro mafi girma a tarihi, bai zama kanun labarai a kafofin watsa labarai na Yammacin duniya, maimakon haka ma sai aka

Share

Dubban masu ziyarar Arbaeen suna tafiya zuwa Karbala yayin da manyan kafofin yada labaran Yamma ke kauda kai daga taron.


Me ya sa babban taro mafi girma a tarihi, bai zama kanun labarai a kafofin watsa labarai na Yammacin duniya, maimakon haka ma sai aka kauda kai a kansa ta hanya mai ban mamaki?

2
Kimanin masu Ziyara miliyan 20 ne suka halarci taron Arbaeen a kasar Iraki a makon da ya gabata.

3
Wannan taro na shekara-shekara, tunawa ne da Imam Husain jikan Manzon Allah, wanda yayi shahada a shekara ta 680 miladiyya, tare da sahabbansa 72, wadandasuka tsaya tsayin daka a gaban azzalumin sarki mai fada da adalci, inda suka sadaukar da rayukansu da na iyalansu ba tare da sun mika wuya ba.

4
Tun makonni biyu kafin ranar Arbain, mutane kasar Iraki suke fara tarbar baki, suna bayar da komai kyauta ga baki: abinci, wurin kwana, ayyukan kula da lafiya da sauransu …

5
Bisa burin ganin sun yi hidima ga mabiyan tafarkin Imam Husaini, da kuma fatan cewa wata rana za ta zo wadda duniya za ta gyaru kuma dan adam ya kubuta daga kangin zalunci.

6
A bisa tsarin jari-hujja na turawa wanda a yau a kansa ne ake tafiyar da duniya, kudi su ne ma’anin kowace mu’amala.

7
Amma a nan, mutane miliyan 20 sun taru don tabbatar da cewa sadaukarwa, tabbar da adalci da girmama dan’adam su ne ma’auni.

8
Sabanin ra’ayin da ya ginu a kan abin duniya da son rai da kuma taskace dukiya, tawagogi na masu ayyukan sai da hidima a Iraki, suna bayar da komai kyauta ga miliyoyin baki masu Ziyara.

9
Wanda hakan ke tayar da hankulan gwamnatocin yamma, kuma kafofin yada labaransu suna kokarin rufe wannan labari, domin zai rusa mahangarsu wadda ta ginu a kan raba dan adam da tunanin addini.

10
Tabbas taron Arbaeen alami ne na addini da ke tara miliyoyin mutane bisa manufa ta addini, wanda ke kara karfafa ruhinsu da kuma Sanya tausayi da jin kan dan adam a cikin zukatansu.

11
Wasu manazarta sun yi imanin cewa ‘yan jari-hujja na Yamma suna matukar tsoron taron Arbain, domin yana gabatar da wani tsari ne na daban da tsarin Yammacin duniya, wanda ya ginu a kan abin duniya kadai da son rai, da kuma Sanya kudi su zama su ne ma’auni a kan duk wani lamarin dan adam, tare da rusa ruhinsa ta hanyar nisantar da shi daga addini.

12
Taron Arbain da alama dai shi ne abu mafi ban mamaki a duniyarmu ta yau wanda kafofin yada labarai ke kawar da kai a kansa, wanda ake rufe baki a kansa ta hanya mai ban mamaki.

13
Za a iya cewa watakila suna Kallon taron Arbain ba wai tattaki ne ba kawai, wani sabon lamari ne da zai iya sauya tunanin dan adam daga tunanin da aka dora shi a kansa a tsawon tarihi.