- Me yasa Ayatollah Khamenei bai cimma yarjejeniya da Amurka ba?
- Domin kaiwa ga amsar, bari mu fara duba tsarin da ya kafa don manufofin kasashen waje.
- Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, tsohon Jagora na kasar Iran, ya sha nanata cewa ya kamata manufofin kasashen waje su dogara ne akan ka’idoji uku: “mutunci, hikima, da kuma maslaha.”
- Wadannan ka’idodi uku, a zahiri sun kunshi taswirar hanya da ke bayyana matsayinsa ga Amurka.
- Ka’ida ta farko ita ce “mutunci,” wacce ke da alaka kai tsaye da yanayin ‘yan siyasar Amurka. A mahangar Ayatollah Khamenei, dabarun Washington a zahiri suna a matsayin na ci gaba ne, amma mai cutarwa.
- Amma Amurka ta janye daga yarjejeniyar a shekarar 2018.
- A mahangar Ayatollah Khamenei, mutunci yana nufin rashin amincewa da dangantaka wadda wani bangare zai iya yin watsi da alkawuransa a kowane lokaci ya ga dama.
- Ka’ida ta biyu ita ce “hikima,” wadda ke da alaka da halayensa na juyin juya hali da kuma zurfin nazarin tarihi. A matsayinsa na wanda ya kasance a cikin yanayin gwagwarmaya tsawon shekaru, Ayatollah Khamenei yana gogewa da masaniya sosai, kuma ya san yanayin halayyar Amurka da take maimaitawa wajen mu’amala da wasu kasashe.
- Daga juyin mulkin 18 ga Mordad a kan gwamnatin Mossadegh ta Iran zuwa juyin mulkin da aka yi wa Pinochet da wasu misalai da dama, da kuma goyon bayan Amurka ga masu mulkin kama-karya a duniya.
- Daga wannan mahangar, an san Amurka a matsayin mai yaudara.
- A mahangar Ayatollah Khamenei, bisa ka’idar hikima Amurka tana bukatar ta dauki darussa daga abubuwan da suka gabata, domin kada ta sake komawa fage yaudarar wasu da sabbin alkawura.
- Ka’ida ta uku ita ce “maslaha,” wadda ake fahimta ta hanyar lura da makomar kawayen Amurka na kud da kud. Shugaban Iran ya ga yadda Washington ta kan yi watsi da abokanta, kamar kawayenta Larabawa, gwamnatocin Turai, da wasu kasashen Asiya, tana raunana ikonsu, a wata ma’ana, tana mayar da su “masu yi mata hidima kawai.”
- Ƙasashe suna sayen makamai na biliyoyin daloli amma ba ta ba su damar yin amfani da su daidai da muradun kasashensu. A mahangarsa, wannan ya yi hannun riga da muradun kasa mai cikakken ‘yanci.
- A karshe, watakila batu mafi zurfi shine fassarar Ayatollah Khamenei a cikin ayoyin Alkur’ani game da yanayin ikon Amurka. Ya bayyana gwamnatin wannan kasa musamman a matsayin “azzaluma” wadda kur’ani ke bayyana ta a matsayin mai son bautar da wasu.
- A cikin wannan nazarin, Amurka ita ce Fir’auna ta wannan zamani, ba ta neman abokin tarayya bisa daidaito, sai ta mayar da masu biyayya a gare ta, ta hanyar nuna karfi musu ƙarfi.
- Saboda haka, ba za a iya tsammanin yin sulhu da Amurka daga wani mutum irin wannan ba. Shi da kansa ya fadi cewa, “Babu amfanin yin shawarwari da Amurka; dalili shine sanin halayenta.”