Yaki da Leken Asiri

Ta yaya Iran ke gano wuraren ajiyar makaman Amurka da ake dauka a matsayin sirri? Rahoton ya yi nazari kan rawar tauraron dan Adam, bayanan

Share

Tutar Iran, taswirar Yammacin Asiya da kwamfuta mai nuna wuraren sojin Amurka


1
Wane ne ke ba Iraniyawa bayanan sirrin wuraren ajiyar kayan yaki na Amurka a Yammacin Asiya? Wannan ita ce tambayar da ake maimaitawa a cikin firgici a cibiyoyi da dama na Washington da Tel Aviv!

2
Makon da ya wuce, Iran ta kai hare-hare na musamman masu ban mamaki a wuraren da ake zaton dukkansu na sirri ne.

3
Nan da nan, wasu kafofin watsa labarai na Yamma suka nuna yatsan zargi a kan Rasha cewa: «Tabbas Rasha ce ta ba su taswirorin.»

4
Amma hanyar sadarwar leken asiri ta Iran ta fi sarkakiya fiye da hanyoyin hadin gwiwa da kawance saboda:

5
Na daya: Tsohuwar hanyar sadarwa da bin diddigi ta asali.

6
Iran, tare da shirinta na makamai masu linzami, ta shafe shekaru da yawa tana habaka dabarun leken asiri ta hanyoyi na zamani, da tattara bayanai cikin tsari na fasaha.

7
Magana ce game da wata hanyar sadarwa ta musamman mai sarkakiya da kwarewa; da suka hada da sanya ido kan hanyoyin samun bayanai na daidaikun mutane a yammacin turai, hotunan tauraron dan adam na kasuwanci, har zuwa nazarin yanayin zirga-zirgar jiragen dakon kaya.

8
Wannan sakamako ne na wani shiri mai alaka da rumbun tattara bayanai da Iraniyawa suka kirkira a shekarun da suka gabata.

9
Na biyu: Wasu boyayyun Kwayenta a yankin da ba a san da su ba.

10
Ƙasashen da suke bayyana adawa da hare-haren Iran, amma a hakika ba su da wata damuwa idan an kawar da wadannan sansanonin. Domin kasancewar rubunan ajiyar kayan yaki na Amurka a cikin kasashensu ya sanya karfin ikonsu a cikin kasashensu ya zama abin tambaya.

11
Na uku: Idanun jama’a.

12
Al’ummar Iraki, Kuwait, Oman, Siriya, har ma da Jordan, sun gaji da shigar da kasashensu a cikin tsarin soji da ke karkashin kasashen waje.

13
Wannan ne ya sa idanuwa da kunnuwan jama’a ke kan kowane dan karamin motsi na ayarin motocin.

14
Daga kwararrun likitoci zuwa ma’aikata a sauran bangarori duk suna shiga cikin wannan aiki na sirri.

15
Na hudu: Makiyan Amurka na duniya.

16
Iraniyawa ba sa yin kasa a gwiwa wajen nadar bayanai ta hanyar daukar sautukan maganganu na jama’a, yanayin zirga-zirgar jiragen dakon kaya, hotunan tauraron dan adam, da kuma bibiyar hanyoyin sadarwa don tunkarar makiyansu.

17
Don haka, amsar tambayar ita ce: sanin sirrin wadannan wurare sakamako ne haduwar tunani da kirkira da kuma aiki tukuru na Iran, hadin gwiwa da amintattu na yankin, da kuma wasu kasashe masu ‘yancin siyasa da suke adawa da mulkin mallaka. Ba a gano wuraren ajiyar kayan yakin Amurka ta hanyar cin amana ba, sai dai ta hanyar wani kawance mai sarkakiya.