Me ya faru ne bayan shudewar watanni 6 ba zato ba tsammani sai kawai aka ga an watsa wata hira mai cike da cece-kuce da wani matukin jirgin Amurka? A makon da ya gabata, aka wallafa wata hira mai cike da cece-kuce, wanda hakan ya tayar da muhawara mai zafi a duniyar labarai
2
Tashar CBS ta America ta watsa wata hira da wani matukin jirgin sama na yaki da aka harbo jirginsa a cikin Iran; matukin jirgin da aka yi wa lakabi da “Bravo” wanda ya yi ikirarin cewa jirginsa ya fadi a gudun kilomita 110 zuwa 160 a kowace awa,
3
Ya samu karaya a Kashin bayansa, hannunsa da kuma kafadarsa, amma a cikin wannan yanayin ya samu damar tafiya kan dutse mai tsawon ƙafa 7,000 don tserewa.
4
Labari mai ban mamaki wanda kafofin watsa labarai na Yamma da masu amfani da kafofin sada zumunta suka yi ta yin shagube a kansa.
5
Babbar tambayar ita ce: me yasa sai bayan watannin 6 ne ake fitar da bayanai kan irin wannan lamari mai kama da Shirin Hollywood? Akwai abubuwan da dole ne a yi la’akari da su. Na farko, rushewar hanyoyin bayanan sirri na soja.
6
A lokacin, Iran ta kai hari kan jiragen yaki da dama, ciki har da jiragen F-15, F-35, da A-10, inda ta harbo wasu a karon farko a tarihin duniya;
7
A lokacin ne Amurka ta yi ikirarin cewa ta karbe cikakken iko da sararin samaniyar Iran da kuma rusa tsarin tsaron sararin samaniyar kasar.
8
A harin Operation Tabas 2, an harbo jiragen sama na Amurka fiye da guda 8, kuma an bayyana sabbin rahotanni kan asarar da Washington ta yi kowace rana. Abin fahimta a nan shi ne cewa, ana son a yi amfani da kafofin yada labarai har ma da salo irin na fina-finan Hollywood, don mayar da shan kaye zuwa nasara.
9
Na biyu – rikita-rikitar zabe. Amurka na gab da gudanar da zaben tsakiyar wa’adi na Majalisar Dokoki.
10
Kuri’un jin ra’ayi sun ce kashi 73% na Amurkawa sun yi imanin cewa Trump bai kula da matsalolin kasarsu ba; kashi 67% suna adawa da harin soja kan Iran, kashi 74% kuma sun ce babu wani abu takamaimai da yake son cimmawa a wannan yaki.
11
Goyon bayan Trump ya ragu hatta a tsakanin ‘yan jam’iyyar Republican, kuma ‘yan Democrat ne ke kan gaba a ra’ayin jama’a kan zaben majalisar dokoki.
12
Dangane da nuna jarumta kan ceto matukin jirgi, wannan yana daya daga cikin yunkurin Trump na neman kuri’u a gaban akwatin zabe.
13
Na Uku — Mummunan Mafarkin Teku. Gwamnatin Yemen mai adawa da Isra’ila ta kwace iko da mashigar Teku a Bab al-Mandab a cikin tekun Red Sea, a wani harin martani mai kama da walkiya.
14
Ta wannan Mashigar ruwan ne ake wucewa da kusan kashi 12% na kayan kasuwanci na duniya, da kuma kashi 11% na dukkanin danyen man fetur na duniya. Farashin mai ya zarce dala 100, kuma farashin dizal na Amurka ya kai matsayi mafi tsada.
15
Washington ala tilas ta shiga wata tattaunawa ta sirri da kungiyar Ansarullah a Oman.
16
Yanzu Amurka tana cikin halin tsaka mai wuya a Iran da Yemen, tana son karkatar da ra’ayin jama’a daga mummunan mafarkinta a teku zuwa wani wasan kwaikwayo na Hollywood a sararin samaniyar Iran.
17
A karshe, shin a nan gaba ma za mu sake ganin wani fim mai ban mamaki na Hollywood a gaban akwatunan zabe?