Wata hira da aka ce an yi ta a shekara ta 2010 domin sanya duniya ta hada kai wajen matsa lamba a kan Iran. Amma akwai wata karamar matsala guda daya: a zahiri ba a taba yin wannan hirar da matar da aka ce an yi hirar da ita ba!
2
Saeed Kamali Dehghan ya mika wa jaridar The Guardian wani rahoto da ya ce ya kunshi hirar da aka yi da wata ’yar kasar Iran mai suna Sakineh Ashtiani, kuma The Guardian ta wallafa rahoton.
3
Ana gab da jefe Wata ’yar kasar Iran da duwatsu !
4
Yanzu bayan shekaru 16, wannan dan jaridar da kansa ya amsa cewa ya kirkiri wannan hirar ne domin amfani da ita wajen tunzura duniya a kan Iran ta fuskar yada labarai.
5
A cikin hirar da aka kirkira, Sakineh Ashtiani ta yi magana kan yanayin da take ciki a gidan kaso, hukuncin da aka yanke mata da kuma wasu bayanai na musamman wadanda babu wanda ya taba sani. Duniya ta kadu sosai da jin hakan.
6
’Yan siyasar kasashen Yamma suka fito suka bayyana matsayinsu, fitattun mutane suka fara kamfe, sannan Iran ta zama wani alami da ake dangantawa da cin zarafin mata.
7
Amma yanzu wannan dan jarida yana fadin cewa: “Ba a taba yin wannan hirar ba.”
8
Babu wani mai shiga-tsakani, babu wata majiya, babu wata murya daga gidan yari. Duk labarin an kirkire shi ne kawai domin wata manufa guda daya:
9
Tsoratar da duniya game da Iran, haifar da kyamar IIran.
Kuma wannan ma ba komai ba ne face wani dan bangare ne kawai na labarin…
10
Bari mu koma watanni tara a baya. Kafofin watsa labaran da suka shafe shekaru 16 suna sake yada wannan karyar tare da Netanyahu da Trump, sun yi ta karawa da cewa a lokacin hargitsin da ya faru a ranakun 8 da 9 ga Janairu, gwamnatin Iran ta kashe mutane 30,000.
11
Alhali bayanai da aka tattara tare da hotunan bidiyo sun nuna cewa ’yan bindigar da aka dauka haya, wadanda suka yi amfani da zanga-zangar matsin tattalin arziki a matsayin wata dama, sun kashe Iraniyawa 2,427 ta hanyar kisan gilla.
12
Marjaneh Satrapi, ita ma ta rasu a wannan shekara; ita ce marubuciyar littafin Persepolis, wadda ta kwashe sama da shekaru goma tana nuna wa Turawa wata mummunar sura mai duhu game da Iran, tana nuna kasar a matsayin kasar da tsananin nuna kyama da kiyayya ga mata, har ta samu lambobin yabo da dama daga turawa kan hakan.
13
Shekaru da suka gabata, wadannan kafofin watsa labaran sun kuma yada wata karya mafi ban mamaki: cewa Ana tilasta wa mabiya addinai marasa rinjaye a Iran daura wata Alamar addininsu a hannunsu!
14
Wani abu ne da bai taba faruwa ba, amma aka rika yada shi a matsayin hujjar cewa ana take hakkin bil’adama a Iran.
15
Kuma akwai wasu daruruwan wasu abubuwa masu ban mamaki irin wadannan, duk ana amfani da su wajen bata sunan kasar.
16
Tsarin farfagandar dai a fili yake:
17
Na farko: a rusa martabar Iran ta hanyar nuna surarta a matsayin kasa marar tausayi ko rashin mutunta hakkin dan adam.
Na biyu: a ba da hujjar matsin lamba, takunkumi, har ma da yaki, ta hanyar gamsar da ra’ayoyin mutane a duniya.
Na uku: a hana Iran zama abin koyi.
18
Domin idan har wata kasa mai cin gashin kanta wadda ba ta dogara da kasashen Yamma ba, za ta iya tsayawa da kafafunta, ta gina kanta da al’ummarta, to kuwa karfin kasashen Yamma wajen tsara labari da dora duniya kan manufofinsu zai fara rugujewa. Sannan al’ummomin da ake ganin sun tasirantu da turai, za su fahimci cewa she akwai wata hanya daban da za a bi, ba dole sai da turawa ba.
19
Amma yanzu lokacin da daga cikin masu kirkirar karya ya fito ya fallasa kansa da kansa, babbar tambayar ita ce: Makaryata nawa ne yanzu suke kan layi don fitowa su fallasa kansu game da labaran karya da suka yada a kan kasar?