Manzon Allah

Gano hakikanin tarihin Manzon Allah Muhammad da koyarwarsa kan rahama, adalci, ilimi, hakkin mata da mutuncin dan Adam.

Share

Masallacin Annabi da Alkur’ani cikin hasken safiya, alamar rahama da koyarwar Manzon Allah Muhammad.

1
Da za a ce mini wani shugaba wanda aka yi masa zalunci mafi muni tsawon shekaru 13 ya yafe wa dukkan abokan gabansa bayan ya ci babban birnin ba tare da zubar da jini ba, da na ce wannan dole ne ya zama labarin fim. Amma wannan shine labarin wani mutum da kafofin watsa labarai suka bayyana surarsa a matsayin wani mai son zubar da jini.

2

Tsawon shekaru, surar Annabi a kafofin watsa labarai na Yamma ta kasance haka: Annabin tashin hankali, Annabin takobi, Annabin da bai ya kallon mace da kima, Annabin jahilci, Annabin da ya zo domin yaki ya haifar da kiyayya.

3
Amma me tarihi da tsoffin rubuce-rubuce suka ce? Bari mu dan duba wasu abubuwa kadan da suka zo a tarihi.
4
A cikin al’ummar da ya kasance bawa, ya daga Bilal dan Habasha har ya zama mai kiran Sallah a Madina.
5
A cikin al’ummar da ke  binne ‘yan mata da ransu, ya sumbaci hannun ‘yarsa ya ce: “Fatima wani bangare ne na jikina”
6
Ya sanya mata su zama masu gado, masu hakkin zabar mazan aure, ya kuma ce: “Mafi kyawu a cikinku shine wanda ya fi mutunta mace.”
7
Amma a lokacin da ya ci Makka kuma kowa yana jiran daukar fansa a kan wadanda suka azabtar da shi, ya fadi wata jimla daya kawai: “ku tafi ku masu ‘yanci ne.”
8
Kuma batun adalci fa?  Wata mata da ta kasance daya daga cikin manyan mutanen Madina ta yi sata. Sai manyan mutane su suka nemi da a kyale ta. Wannan yasa ya yi fushi ya ce: “ta yaya Zan hukunta marasa karfi in bar manyan mutane su tafi?!  Ina rantsuwa da Allah, idan da  ‘yata za ta  yi sata, zan hukunta ta.”
9
A Yaƙin Madatsar Ruwa, shi da kansa ya yi aiki tare da ma’aikata. A cikin Madina yana zama a ƙasa kamarsauran mutane ma’aikata.
10
Ya kan jaddada bukatar amfani da hankali, koyo, da taimaka wa wadanda aka zalunta.
11
Amma babban sakonsa abu daya ne: Kai mutum, ba ka zo wannan duniya ne domin zama da shantakewa ba, an halicce ka ne domin ka jurewa Jarabawa da wahala, da hakuri, da kuma yin abin da ya dace domin samun sakamako mafi girma, da aljanna madawwamiya.

12
Akwai bayanan tarihi da yawa game da shi.
13
Amma tambayar a yau ita ce: Me yasa suka bata shi tsawon shekaru da yawa?
14
Me yasa suke fadin karya da yawa game da shi, game da littafinsa mai tsarki wato Alƙur’ani, a hali yana  yana kiran mutum ne zuwa ga tausayi, adalci, aiki da hankali?  Me yasa suke yawan nuna surar batunci a kansa?
15
Shin suna jin tsoron adalci ne? Shin suna jin tsoron rufe masana’antar makamai da cinikin kayan yaki ne?
16
Shin suna damuwa game da rugujewar manyan kamfanoninsu ne? Shin suna jin tsoron wargaza tsarin barna, gidajen caca, da sabbin hanyoyin bautar da mutane da shahaltar da su da hanyoyin nishaɗi na yanar gizo?
17
Da alama a yau muna bukatar sake sanin Wane ne manzon Allah Muhammad.