Kungiyar agaji ta red crescent ta iran da kuma kungiyar red cross ta kasar Saliyo sun cimma yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu.
An cimma wannan ne a yayin ziyarar da babban daraktan kula da lafiya na kungiyar agaji ta Red Crescent na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai Saliyo tare da gudanar da tarurruka da dama da shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar.
Bayan taron, an rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kungiyar agaji ta Red Crescent ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kungiyar agaji ta Red Cross ta Saliyo a ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Saliyo.